Ga dukkan alamu masu karfin gaske, sanatocin jam'iyyar APC
sun sake matsa lamba tare da huro wuta ta tsige Abubakar Bukola Saraki daga
mukamin sa na shugaban majalisar dattawa sakamakon aukuwar sauye-sauyen sheka
zuwa jam'iyyar PDP cikin wannan mako.
'Dan Majalisar na jam'iyyar APC mai wakilcin mazabar jihar
Katsina ta Kudu, Sanata Abu Ibrahim, shine ya yi ambaton hakan a ranar Alhamis
din da ta gabata yayin ganawa da manema labarai dangane da sauyin shekar Saraki
zuwa jam'iyyar PDP cikin wannan mako. Abu Ibrahim ya jaddada cewa, Sanatocin
jam'iyyar APC su ne mafi rinjaye a majalisar dattawa saboda haka babu wata
hanya da za ta ba da dama ga tsintacciyar mage ta ci gaba da jagorantar su.
A cewar sa, dole ne Saraki ya yi murabus daga kujerar sa ta
shugabancin majalisar dattawa muddin zaman lafiya da kwanciyar hankali za su ci
gaba da dorewa a cikin ta dangane da nasaba ta kasar nan da kuma dimokuradiyya.
Sanata Ibrahim wanda shine shugaban kwamitin harkokin
jami'an 'yan sanda na majalisar, ya kuma bayyana cewa, akwai yiwuwar majalisar
za ta dakatar da hutun ta kafin ranar da ta kayyade na dawowa sakamakon doka da
ta bayar da dama ga 'yan majalisa 30 su warware wannan hukunci na hutu a kowane
lokaci.
NAIJ.com ta ruwaito cewa, bayan jagorantar zaman majalisa a
ranar Talatar da ta gabata inda guguwar sauyin sheka ta kada a cikin ta, Saraki
ya kuma bayar da sanarwar afkawar majalisar shiga hutu har zuwa ranar 26 ga
watan Satumba.
A baya can, sanatan mai wakilcin jihar Katsina ta Kudu ya
nemi Saraki akan ya fice daga jam'iyyar ta APC sakamakon ruwa da tsakin da ya
yi wajen ficewar Sanatoci 14 da kuma 'yan majalisar wakilai 37 daga jam'iyyar.
Rahotanni sun bayyana cewa, a baya shugabancin jam'iyyar APC ta fara gudanar da
shirye-shiryen korar Saraki daga jam'iyyar sakamakon rawar da ya taka wajen
assasa guguwar sauyin sheka a ranar Talatar da ta gabata.
Sai dai Sanata Ibrahim ya yabawa Saraki dangane da ficewar
sa daga jam'iyyar da cewar huta roro, kuma a halin yanzu murabus kadai ya rage
ma sa wanda muddin ba haka to kuwa ba bu sauran zaman lafiya a majalisar
dattawa.
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> whatsapp://chat?code=41x2TuRqdVQ9PrcrucqpTu Latsa nan domin ka sauke Manhajarmu ISYAKU.APK https://docs.google.com/uc?export=download&id=0B7lmLLhGZSx5OTVENFlsTkllRTQ Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira
Hausa.naij.ng