Shugaban karamar hukumar mulki ta Kalgo Alh. Umar Namashaya Diggi, ya ce duk wani ma'aikacin karamar hukumar mulki ta Kalgo da bai karbi katin zabe na kasa ba watau PVC ba zai karbi albashin sa na watan Satumba ba.
Namashaya ya jaddada ma isyaku.com haka yayin wata tattaunawa a garin Birnin kebbi, bayan an jiyo shugan na karamar hukumar Kalgo ya furta wadannan kalamai a wata kafar watsa labarai.
Namashaya ya fayyace dalla-dalla a tattaunawar, dalilin da ya sa ya ce haka, lamari da ya fi dangantawa da kishin kasa da yi wa kai.
Za a rufe yin rijistan ranar 17 ga watan Agusta 2018.
Saurari sautin muryar tattaunawar:
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> whatsapp://chat?code=41x2TuRqdVQ9PrcrucqpTu
Latsa nan domin ka sauke Manhajarmu ISYAKU.APK
https://docs.google.com/uc?export=download&id=0B7lmLLhGZSx5OTVENFlsTkllRTQ
Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com
Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira