Jami’an hukumar Yansandan jihar Gombe sun sanar da cafke
wasu mutane su bakwai da suka kwashe tsawon lokaci suna yi ma wata karamar
yarinya mai kimanin shekaru goma sha hudu fyade, inji rahoton jaridar Aminiya.
Majiyar NAIJ.com ta ruwaito daga cikin mutanen da aka kama, akwai Hamza Musa
wanda a garin lalata da yarinyar ya harbeta da cutar nan mai karya garkuwan
jiki, watau sida ko ace mata Kanjamau, haka zalika binciken Asibiti ya nuna
yarinyar na dauke da juna biyu.
Wannan lamari ya faru ne a unguwar Poli, dake cikin karamar
hukumar Yamaltu Deba, acan ne aka tafka yarinyar nan wannan aika aika, inda
take zuwa yawon talla, kamar yadda mahaifinta mai suna Malam Abdullahi ya
tabbatar. Shi kuwa wannan mutumi da ake zargin harbar yarinyar da cutar
Kanjamau, mai suna Hamza Musa an kama shi ne a ranar Litinin da ta gabata, a
shagonsa dake kasuwar Kwadon, inda yake sayar da alawa.
Mahaifin yarinyar, Malam Abdullahi ya bayyana cewa bayan
wani dan bincike da aka gudanar, sai ga shi an damko wuyar mutane bakwai,
mutanen da bincike ya nuna suma sun yi lalata da wannan yarinyar a unguwar
Poli.
Tuni dai Hamza ya amsa laifinsa, kuma har ma an bada
belinsa, amma da zarar an kammala bincike za’a gurfanar dasu duk gaban kuliyan
manta sabo, kamar yadda wani jami’in ma’aikatar walwala na jihar Gombe ya
bayyana.
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> whatsapp://chat?code=41x2TuRqdVQ9PrcrucqpTu Latsa nan domin ka sauke Manhajarmu ISYAKU.APK https://docs.google.com/uc?export=download&id=0B7lmLLhGZSx5OTVENFlsTkllRTQ Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira
Hausa.naij.ng