Type Here to Get Search Results !

Main event

Allah kadai ne zai iya takawa Buhari burki a zaben 2019 – Masu karatu

Bisa dukkan alamu dai zai yi wahala a samu ‘Dan takarar da zai iya ja da Shugaba Muhammadu Buhari a zabe mai zuwa na 2019. Masu karatun mu ne su ka bayyana mana wannan a jiya ta hanyar zabe.

NAIJ Hausa ta nemi jama’an da ke karanta shafukan ta su zabi wanda su ke ganin zai yi nasara a zaben 2019. Cikin mutanen da su kayi wannan zabe dai kashi 52% sun bayyana cewa babu wanda zai iya ja da Shugaba Buhari a 2019.

Bayan nan kuma an samu kashi 38% cikin wadanda su ka nuna cewa tsohon Gwamnan Kano Rabiu Musa Kwankwaso zai iya ja da Shugaba Buhari. Kason wadanda su ke da wannan ra’ayi ba su kai masu ganin Buhari zai yi nasara ba.

Kashi 6% rak ne kuma su ke ganin cewa tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar na iya takawa Shugaba Buhari burki a zabe mai zuwa. Atiku Abubakar dai ya bayyana cewa idan aka zabe a 2019 sa ba zai nemi tazarce ba.

Kashi 4% kuma su na da ra’ayin cewa Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki zai doke Shugaba Buhari idan aka tsaya takara a zaben 2019. Saraki dai yana kokwanton cewa zai yi takarar Shugaban kasa a shekara mai zuwa a PDP.

Kun ji labari cewa Sanata Ahmad Makarfi ya huro wuta Jam’iyyar PDP ta ba shi dama yayi takara da Buhari a 2019 inda yace kutun-kutun aka hana sa takara a karkashin PDP a zaben 2007.


Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira

Hausa.naij.ng

Top Post Ad

Below Post Ad

Shiga group dinmu na WhatsApp domin samun labaran mu kai tsaye LATSA NAN
Domin zama Wakilin mu a garin ku LATSA NAN
Domin aiko Sako/Labari/Korafi LATSA NAN
Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN
Domin samun labaranmu a Twitter LATSA NAN

Hollywood Movies