Sani Musa Saminaka | Yauri | 12-8-2018 |
Kungiyar Dalibai Musulmi na Najeriya ,MSSN na jahar Kebbi ta kammala taronta da ta keyi na kwana shidda agarin Yauri da safiyar Lahadi.
Taron na bana ya fi mayar da hankali ne a kan fadakarwa da ilmantarwa kan kalubale tare da yadda ya kamata dalibai da matasa Musulmi su fuskanci rayuwa bisa tsarin tarbiyyar Musulunci da ya yi daidai da zamani, ta yadda za su ci gajiyar rayuwa a zamanance a matsayinsu na Musulmi.
A wurin wannan taron angabatarda abubuwa daban-daban
na koyarwa ma su ban shawa , musamman yadda wasu Dalibai suka Mike tsaye
suka bayyana abubuwanda da suka fahimta a wurin gabatarda wannan taron.
Bugu da Kari Dalibai sun gabatarda hikimomi daban-daban a
wurin wannan taron irnsu karatun Alkur'ani, musabaka, Taken addinin Musulunci, da sauransu.
Tafuskar sarauta, Mala.Shehu Yahaya/Shehin Matasa Babban limamin Masallacin jumu'a na mai
martaba sarkin Yauri ,shi ne ya wakilci Sarkin a wurin wannan taron .
Bangaren siyasa kuma an samu halaratar Alhaji Abubakar Sadik Katukan Yauri
Bangaren 'yan kasuwa kuma ansamu halaratar Alhaji Adamu Laka Ciyaman na 'yankasuwar masarautar Yauri baki daya
An samu halartar tsofaffin Prinsipal irinsu Mal.Musa
Ibrahim Mani, hakazalika ansamu halartar wasu daga cikin Prinsipal na yanzu,
Bangaren dalibai kuma, ansamu halartar dalibai da dama daga
sassa daban-daban na makarantun sakandare da kuma sama ga sakandarin a
fadin jihar kebbi baki daya.
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> whatsapp://chat?code=41x2TuRqdVQ9PrcrucqpTu
Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com
Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira