Daruruwan matasa a karamar hukumar Hadejia ta jihar Jigawa
sun gudanar da zanga-zangar nuna kin amincewar su da komawar Sanatan su
jam'iyyar PDP. Sanatan yankin, Ubali Shitu, na daga cikin sanatocin da suka
canja sheka daga jam'iyyar APC zuwa PDP.
Matasan sun fara zanga-zangar, duk da ana ruwan sama kamar
da bakin kwarya, daga kamfanin sarrafa rake zuwa fadar sarkin Hadejia inda suke
rera waken neman Sanatan ya yi murabus daga mukamin sa tare da bayyana cewar
"duk wanda ba ya son Buhari barawo ne." Matasan na dauke da takardu
da rubutattun sakonni da suka hada da "bamu yarda da yaran Saraki
ba", "duk mai akidar sata ba zai zauna inuwa daya da Buhari ba",
"Buhari muke kauna ya zarce har 2023".
Akwai rashin jituwa tsakanin Sanata Ubali Shitu da gwamnan
jihar Jigawa, Badaru Abubakar. Sanatan ya ci al washin tabbatar da ganin gwamna
Badaru bai sake cin zabe ba a 2019. Shugaban masu zanga-zangar kuma na hannun
dama ga gwamna Badaru, Bala Umar, ya shaidawa manema labarai cewar sun yi hakan
ne domin tabbatarwa duniya cewar Sanata Ubali ba da yawun jama'ar da yake
wakilta ba ya koma PDP.
"Lokacin da yake
jam'iyyar APC zaka samu mutane tare da shi duk lokacin da ya zo Hadejia amma
tunda ya koma PDP ba ya iya shigowa Hadejia sai a sace saboda tsoron
jama'a," a cewar Umar.
Da aka tuntubi Bala Aji, mai magana da yawun Sanata Ubali,
ya bayyana cewar yana da masaniyar zanga-zangar amma ba zai iya cewa komai a
kai ba har sai ya tuntubi maigidan nasa. Sanatan ya gaza samun sukuni a garinsa
na Hadejia tun bayan komawar sa jam'iyyar PDP domin ko a yau sai sulalewa ya yi
daga garin ya gudu Kano.
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> whatsapp://chat?code=41x2TuRqdVQ9PrcrucqpTu
Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com
Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira
Hausa.naij.ng
Tags:
LABARI