Hukumar yaki da masu cin hanci da rashawa ta kasa EFCC ta
kai sumame gidan tsohon shugaban hukumar jami'an tsaro na farin kaya SSS.
Jami'an hukumar sun isa gidan tsohon shugaban hukumar ne
Mista Ita Ekpeyong da yammacin yau Alhamis, wanda ake tsammanin an turo su ne
bisa umarnin mukaddashin shugaban kasa Yemi Oeinbajo.
Mista Ekpeyond ya jagorancin hukumar tun daga shekara ta
2010 zuwa shekara ta 2015 kafin shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sauke shi
tare da nada Lawan Daura, wanda shi ma aka tunbuke shi a cikin satin nan.
Daga cikin kadarorin da ake kokarin yin bincike akansu akwai
wani gida dake Asokoro a Abuja. A shekara ta 2017 an yi yunkurin yin hakan amma
har ta kai ga sabani tsakanin jami'an hukumar farin kayan da kuma jami'an
hukumar EFCC, kafin daga bisani Lawan Daura ya shiga cikin maganar tare da hana
aikata hakan.
Hukumar tana zargin Mista Ekpeyond akan siyan wasu makamai
ba bisa ka'ida ba tare da karkatar da akalar wasu kudin makamai wadanda aka
cire domin yaki da ‘yan tada kayar baya na Boko Haram. Sai dai ya zuwa yanzu
babu wanda zai iya bayyana cewa wannan sumame da hukumar EFCC ta kai yana da
nasaba da cigaba da wancan zargi da ake masa tun shekara ta 2017.
Mai magana da yawun hukumar ta EFCC Wilson Uwujaren baya
daga kira balle majiyarmu ta ji ta bakinsa game da lamarin, amma duk da haka an
aike masa da sakon kar ta kwana ko in anyi sa’a ya biyo baya.
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> whatsapp://chat?code=41x2TuRqdVQ9PrcrucqpTu
Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com
Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira
Hausa.naij.ng
Tags:
LABARI