Yadda dan Kofar Kola ya kalubalanci kujerar dan Majalisar tarayya, B-kebbi,Kalgo,Bunza

Yayin da Kalangun Siyasa ya fara kadawa a jihar Kebbi gabanin zaben 2019 hakazalika wasu yan siyasa sun fara taka rawa. Bisa wannan rawar ce wani haifaffen Kofar Kola daga tsakiyar garin Birnin kebbi watau Alh. Abu Najakku ya kalubalanci kujerar Dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Birnin kebbi, kalgo da Bunza.

To amma miye hujjojin da Najakku ya dagara da su domin kalubalantar kujerar dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Birnin kebbi, Kago da Bunza ?.

A cikin kalamansa na neman zabe a garuruwa da ya ziyarta domi neman amincewar jama'ar Mazabar da zai wakilta da suka hada da Kalgo, Badariya Magarza, Gayi Dangoma, Diggi, Kuka ,Nayelwa da Zuguru kawo yanzu a zagayen farko, Abu Najakku ya ce " Jama'a ina son ku sani, lokaci ya wuce wanda za ku sha wahala ku zabi Dan Majalisa ya je Abuja ba za ku sake ganinshi ba sai wani lokacin zabe. Yana shigowa yana fita kuma yana karbar Miliyoyin naira amma bai iya yi maku komai".

A garin Zuguru, wani mai suna Muhammed Karina ya ce " Tun lokacin da suka zabi wani dan siyasa a 2015 zuwa Majalisar tarayya, wannan dan siyasa bai sake waiwayarsu ba, sakamakon haka su kam sun aminta da irin yadda Najakku ya gabatar da kanshi tare da la'akari da tarihi da labarin halayensa tun kafin ya fito siyasa".

Ya kara da cewa shi fa idan aka zabeshi, zai yi amfani da tsintsiya ya share wadanda ke yi wa shugaba Buhari tsageranci a cikin Majalisa, tallafa wa matasa da sana'oi domin su dogara da kansu, inganta sana'oin hannu, bunkasa ilimi, kuma zai bayar da ingantaccen wakilci kasancewa ya yi karatu gwargwado, kuma ya dangana ilimin wasu fannoni na rayuwa, kuma ga shi dama dan Jarida ne kwararre.

Yanzu haka, Abu Najakku yana ci gaba da yin rangadin garuruwa da ke karkashin wakilcin kujerar da yake nema na Dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Birnin kebbi, Kalgo, da Bunza a karkashin jam'iyar APC.

Ku kasance tare da mu domin jin cikakkaen manufofin Abu Najakku ga jama'ar Birnin kebbi, Kalgo da Bunza a rahotun mu na gaba.

Daga sashen Siyasa na isyaku.com

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> whatsapp://chat?code=41x2TuRqdVQ9PrcrucqpTu
Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com
Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN