Tsohon gwamnan jihar Kaduna Alhaji Balarabe Musa ya bayyana
cewa ficewar shugaban majalisar dattawa Dakta Abubakar Bukola Saraki daga
jam’iyyar APC zuwa jam’iyyar PDP zai kawo nakasu ga nasarar shugaba Muhamm ad
Buhari a kakar zaben shekarar 2019.
Tsohon gwamnan ya bayyana hakan ne a cikin wata ganawa da ya
yi da manema labarai a jiya Talata, inda ya jaddada cewa babu shakka ficewar
Sarakin za ta kawo tangarda tare da kawo cikas ga shugaba Muhammad Buhari tare
da jam’iyyarsa ta APC a zaben 2019. Idan za'a iya tunawa dai a ranar Talata ne
dai shugaban majalisar dattawan ya fice daga jamiyyar APC zuwa jam’iyyar APC
zuwa jam’iyyar PDP.
"Ficewar Bukola Saraki daga jam’iyyar APC ya sanya
jam’iyyar cikin rudani, domin kai tsaye karshen jam’iyyar ya zo". A cewar
Balarabe Musa. Sannan ya kara da "Babu Shakka abubuwan da za su biyo baya
bayan ficewar Saraki daga jam’iyyar APC, ba zai haifarwa da jam’iyyar da mai
ido ba. Domin zai kawo cikas ga nasarar jam’iyyar a zabe mai zuwa".
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> whatsapp://chat?code=41x2TuRqdVQ9PrcrucqpTu Latsa nan domin ka sauke Manhajarmu ISYAKU.APK https://docs.google.com/uc?export=download&id=0B7lmLLhGZSx5OTVENFlsTkllRTQ Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira
Hausa.naij.ng