Abdulmumin Jibrin Kofa, dan majalisar wakilai mai wakiltar
kananan hukumomi Kiru da Bebeji a jihar Kano, ya yi ikirarin cewar akwai
gwamnonin jam'iyyar PDP 4 dake aiki tare da jam'iyyar APC domin ta kai ga
nasara a zaben 2019. Duk da bai ambaci sunayen gwamnonin ba, Kofa ya bayyana
cewar akwai yarjejeniya tsakaninsu da jam'iyyar APC. Da yake ganawa da manema
labarai a Abuja a jiya, Laraba, Kofa ya ce, "a halin yanzu akwai gwamnonin
jam'iyyar PDP 4 zuwa 5 da aka kulla yarjejeniyar goyon bayan takarar shugaba
Buhari da su a zaben shugaban kasa."
Sannan ya kara da cewa, "jam'iyyar APC ba ta girgiza ba
saboda fitar wasu 'ya'yanta ba." Kazalika ya kara da cewar APC na daukan
matakan ganin cewar ta cigaba da juya siyasar jihohin da take da yawan magoya
baya.
"Da a ce wani dan takarar APC ta tsayar ba shugaba
Buhari ba, da sai na dan ji raina ya sosu saboda ficewar wasu 'ya'yan jam'iyyar
amma yanzu bana jin ko dar a raina saboda shugaba Buhari ke yiwa APC takarar
shugaban kasa. "Duk masu sukar Buhari da canja sheka 'yan siyasa ne da
basu da wasu jama'a, a saboda haka zaben 2019 zai kasance ne tsakanin 'yan
Najeriya da wasu tsirarun 'yan siyasa masu son zuciya," in ji Kofa.
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> whatsapp://chat?code=41x2TuRqdVQ9PrcrucqpTu Latsa nan domin ka sauke Manhajarmu ISYAKU.APK https://docs.google.com/uc?export=download&id=0B7lmLLhGZSx5OTVENFlsTkllRTQ Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira
Hausa.naij.ng