isyaku.com | 30-8-2018 |
Kungiyar tsofaffin ma'aikata da masu karban fansho na jihar Kebbi, Retired Officers Welfare Association ROWA, ta dage wani addu'a da manbobinta suka so yi a babban Masallacin Idi da ke unguwar Gesse 2 da ke garin Birnin kebbi har zuwa kwana biyu domin ba da sukuni na tattaunawa tsakanin shugabanninta da gwamnatin jihar Kebbi.
Wani jigo a kungiyar, Alh. Babangida Garba Gwandu, Danburam, ya shaida wa manbobin kungiyar haka a filin na Idi.
Alh. Babangida ya ce cikin kwana biyu kacal za su san matsayinsu akan lamarin. Ya kuma bukaci manbobin kungiyar su koma gidajensu, su jira har nan da kwana biyu, wanda kafin wannan lokaci an gama duk wata tattaunawa da bangaren gwamnati.
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> whatsapp://chat?code=41x2TuRqdVQ9PrcrucqpTu
Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com
Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira