Isyaku Garba | 20-8-2018
Kungiyar nan da ke karadin taimaka wa Sanata Adamu Aliero,
mai suna Aliero Suport Organisation karkashin jagorancin Anas Ibrahim Sanusi
Chairman, Shamsu Saidu Aliero Campaign Director , Basiru Muh'd Project
Director, da Najashi Muhd V.Chairman, sun bayar da taimako ga gajiyayyu da
marasa karfi a garin Birnin kebbi, Kalgo, Bunza, Maiyama da Gwandu.
Tawagar ta fara ziyartar gidan Marayu da ke garin Birnin
kebbi da sanyin safiyar Lahadi 18 ga watan Agusta inda ta sallama gidan Marayun
da alherin katon Rago, sai kuma ta bisu da shadda guda biyu da turame guda uku, da buhun shinkafa goma. Amma fa kafin nan, kungiyar ta fara ziyartar unguwar Gesse inda ta bayar da
taimakon buhu goma na shinkafa, shadda goma, buhun shinkafa goma da atamfa
ashirin. Kafin tawagar ta bar garin Birnin kebbi, sai da ta ziyarci Asibitin
Sir Yahaya, ta bi daki-daki ta bayar da taimakon kudi ga bayin Allah da ke
kwance.
Daga garin Birnin kebbi fa sai garin Kalgo, inda tawagar ta
kai ziyaran ban girma tare da neman tuwassali, ta sallama daga bisani yan
tawagar suka fadi suka yi gaisuwa ga Sarkin Gobir na Kalgo Alh. Haruna Jadda
Bashar, nan ne fa uban tafiya Anas Ibrahim Sanusi, ya shaida wa Sarki makasudin
zuwansu. Daga bisani tawagar ta bayar da yadi goma, atamfa goma tare da buhun
shinkafa goma. Bayan wannan ne fa ,Basaraken, ya bayyana farin cikinsa bisa
yadda yan wannan tawaga suka sa tsoron Allah, kuma suka gudanar da wannan
taimako ga gajiyayyu tare da yi masu addu'a tare da Sanata Adamu Aliero, suna
da masu iya magana ke alakantawa da Ainun bushra.
Kafin tawagar ta fice daga garin Kalgo mai tarihin al'adu a
kasar Masarautar Gwandu, sai da ta leka marasa lafiya a cikin Asibitin garin Kalgo, kuma ta sada
marasa lafiya da alherin bazata ta hanyar damka masu kudade a hannayensu a
matsayin taimako.
Daga nan ne fa tawagar ta zarce zuwa garin Bunza, inda a nan
ma ta sami albarkar Fadar Sarkin Bunza Dr. Mustapha Bunza, wanda ya yi ma
tawagar kyakkyawar tarbo tare da mika godiyar jama'arsa ga tawagar da kuma
Sanata Adamu Aliero. A nan garin Bunza ma , tawagar ta bayar da taimakon buhu
goma na shinkafa, shadda goma tare da turmin zane guda ashirin. Bayan Fadar
Sarki, tawagar ta shiga Asibitin garin Bunza, bayan addu'an neman Allah ya
baiwa marasa lafiya sauki, sai tawagar ta bi marasa lafiyan da kunshin kudi
gado zuwa gado kowa ya sami taimakon.
Daga garin Bunza fa tawagar ta yi bankwana da abokan arziki,
aka sha ruwa, aka yi Sallah, sai fa tawagar ta zarce kai tsaye zuwa garin
Gwandu, inda a nan ma ta gabatar da taimakon wanda Ajiyan Sarkin Gabas na garin
Gwandu Alh. Biza ya wakilta, ya yi wa tawagar kyakkyawar addu'a daga bisani
tawagar ta gabatar da buhu goma , atamfa guda ashirin, sai shadda guda goma.,
bayan haka, sai tawagar ta dira Asibitin garin Gwandu, a nan ma ta bi daki-daki
ta raba wa Marasa lafiya kudi hannu da hannu.
Toh fah, ka ji aikin alhairi daga dan alhairi mai tunanin
alhairi, kuma wakili mai mukamin Sanata wanda ke wakiltar al'umar Kebbi ta
tsakiya a Zauren masu fararen gemu na Majalisar Dattwa ta Najeriya watau Alh.
Adamu Aliero, ta hanyar tunani irin na hazikan amintattun matasa masu karadin
ganin nassarar Sanata Adamu Aliero karkashin kungiyar Aliero Support
Organisation.
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> whatsapp://chat?code=41x2TuRqdVQ9PrcrucqpTu
Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com
Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira