• Labaran yau

  An fallasa kasar dake taimaka ma yan shia da makaman kare dangi


  Rahotanni sun fallasa kasar Iran a matsayin kasar dake taimaka ma yan Shi’a da makamai don sun kaddamar da yaki a kasar Iraqi da sauran kasashen dake hamayya dasu, inji rahoton jaridar Daily Trust.

  Majiyar NAIJ.com ta ruwaito kasar Iran na cigaba da karfafa mayakan yan shia dake kasar Iraqi mai suna Quds da makaman kare dangi watau nukiliya don su kare kansu tare da kai ma duk wata kasar dake yaki dasu hari.

  Wani hadakar jami’an gwamnatin kasar Iran guda uku, jami’a leken asiri na kasar Iraqi da wasu jami’an kasashen turai ne ta bayyana haka, inda tace a yanzu haka Iran ta aika da makaman nukiliya masu kananan zango ga yan shi’ar kasar Iraqi a watannin da suka gabata.

  Haka zalika wasu jami’an leken asiri guda biyar sun tabbatar da cewar Iran na taimaka ma yan shi’an Iraqi da kayan aiki domin su fara kera makamansu da kansu. “Hikimar yin haka shine don Iran ta samu tufun dafawa idan har an kai mata hari. “Nukilyan da ta baiwa yan shi’an basu dayawa, basu wuce dozin daya ba, amma zasu iya kara yawansu idan bukatar haka ya taso.”

  Inji wani jami’in kasar Iran. A baya kasar Iran ta sha yin ikirarin cewa makaman nukiliya da take kerawa zata yi amfani dasu ne kawai idan an tabata, amma sai ga shi da aka tambayi manyan jami’an kasar game da wannan batu sai suka zuke, suka ki cewa uffan.

  Daga cikin makaman da yan shi’an kasar Iraqi suka samu akwai wasu nukiliyoyi masu suna Zelzal, Fateh-110, da Zolfaqar wanda zasu iya kai nisan kilomita 200 zuwa 700, wanda hakan ya sanya kasashen adawar Iran Isara’ila da Saudiyya cikin wannan zango.
   

  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> whatsapp://chat?code=41x2TuRqdVQ9PrcrucqpTu Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira

  Hausa.naij.ng
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: An fallasa kasar dake taimaka ma yan shia da makaman kare dangi Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });