Buhari 2019: Kungiyar BOCA reshen jihar Kebbi ta canja shugabanninta na jiha

Kungiyar da ke karadin gani shugaba Muhammadu Buhari tare da mataimakinsa Yemi Osinbajo sun sake tsaywa takar a 2019 Buhari Osinbajo Continuity Agenda BOCA 2019 reshen jihar Kebbi, ta canja shugabancin kungiyar inda ta zabi Alh. Mainassara Katanga Garkuwan Maiyama a matsayin sabon shugabanta na reshen jihar Kebbi, a wani tarao da ta yi ranar Laraba 15 ga watan Agusta 2018 a garin Birnin Kebbi .

Sauran sune Alh. Zubairu Dankanawa Mataimakin shugaba na jihar Kebbi, Alh. Shehu Shanga mataimakin shugaba, Alh. Abubakar S. Aliyu Sakataren kungiya.

Alh. Mainassara, ya karbi ragamar shugabancin kungiyar ne daga hannun tsohon shugabanta Alh. Muhammad Dantila, bayan amincewa daga exco na kungiyar guda 23 cikin 37.

Majiyarmu ta shaida mana cewa, canjin shugabancin kungiyar, ya samo asali ne sakamakon wasu matsaloli na cikin gida, haka zalika, majiyar ta shaida mana cewa, an yi haka ne domin a tabbatar da nassara a kan alkiblar da aka fuskanta na ganin kungiyar ta kai ga nassara bisa manufofinta domin ganin cewa shugaba Buhari tare da mataimakinsa Osinbajo sun ci zabe a 2019.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> whatsapp://chat?code=41x2TuRqdVQ9PrcrucqpTu Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN