Tsofaffin ma'aikatan gwamnatin jihar Kebbi sun gudanar da addu'ar neman a biyasu hakkinsu
Kungiyar tsofaffin ma'aikatan gwamnatin jihar Kebbi, watau Kebbi state retired officers welfare Association karkashin jagorancin shugabanta na jihar Kebbi Idris Muhammed Kangiwa, ta gudanar da wani taro a babban Masallacin Idi da ke unguwar Gesse a garin Birnin kebbi ranar Alhamis, inda manbobinta daga ko'ina cikin jihar Kebbi suka sami halarta domin isar da sako ga Gwamnatin jihar Kebbi na bukatar a biya su hakkokinsu na fansho.

Yan fanshon, sun gudanar da addu'oi na neman Allah ya karkata zukatan shugabannin jihar Kebbi a kan su gaggauta biyansu hakkokinsu, duba da irin wahalhalu da suke fuskanta ganin cewa karfinsu ya kare kuma ba'a biya su hakkokinsu ba.

Tun farko dai, jami'in watsa labari na kungiyar PRO Audu Muhamed, ya yi jawabi a kan yadda tsarin shugabancin kungiyar yake, haka zalika ya bayar da dama manbobin kungiyar su fadi korafinsu.

Wata tsohuwar babban ma'aikaciyar gwamnatin jihar Kebbi Dr. Hajara Mairokota Dakingari, ta yi ritaya a 2017, amma har yau ba a kira su ba balle a tantancesu domin a fara biyansu hakkokinsu. Hajara ta nuna rashin gansuwa ga rashin bayyanan shugabannin kungiyar, sakamakon haka ta abukaci a yi gyara.

Hakazalika Malam Musa Lawal, sakataren wadanda suka yi ritaya a 2013 da 2013 a madadin yan kungiyarsa ta yan fansho na 2012 da 2013, ya roki gwaamnati cewa ta yi wa Allah ta biya su hakkinsu da sabon matakin fansho, wanda ya samo asali tun lokacin Gwamna Saidu Dakingari har Gwamna Atiku Bagudu ya gaji matsalar.

Da muka tuntubi wani babban ma'aikacin Gwamnatin jihar Kebbi da lamarin ya shafa, ya shaida mana cewa "Shugabannin kungiyar tsofaffin ma'aikatan ne suka kira jamaa'arsu domin ssu sanar da su zance da aka yi da Gwamnati, amma ba wai wata matsala bace. Kuma zancen kudi ne, za a biyasu matukar an sami kudin".

Saurari sautin wani jawabi a wajen taron:Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> whatsapp://chat?code=41x2TuRqdVQ9PrcrucqpTu Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN