Mun samu labari daga Jaridar Premium Times cewa Majalisar
dinkin Duniya ta bayyana yadda ‘Yan ta’addan Boko Haram da su ka fitini yankin
Arewa maso Gabashin Kasar nan ke samun kudi.
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> whatsapp://chat?code=41x2TuRqdVQ9PrcrucqpTu Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira
Hausa.naij.ng
Talaucin da yayi wa jama’a katutu a Yankin tafkin Chad yana
daga cikin manyan dalilan da su ka sa ‘Yan Boko Haram ke samun Mabiya wadanda
ke kai manyan hare-hare a masallatai da sauran wurare a fadin Arewacin
Najeriya.
‘Yan ta’addan kan yi garkuwa da mutane ko kuma su sace kayan
jama’a domin samun kudin shiga. Wani lokaci na dai ‘Yan ta’addan kan samu
gudumuwa daga hannun wasu boyayyun mutane domin su cigaba da danyen aikin su
Kwamitin tsaro na Majalisar dinkin Duniya watau UN ta gabatar da wata takarda
kwanan nan inda ya bayyana cewa Boko Haram da kuma ‘Yan ta’addan ISIL su kan sace
mutane su yi garkuwa da su domin tatsar kudi daga Bayin Allah.
Kawo yanzu dai ‘Yan Boko Haram sun yi sanadiyyar mutuwar
dinbin mutane a Najeriya musamman a Yankin Adamawa da Borno da Jihar Yobe. Wasu
kungiyoyi masu zaman kan-su su na cikin masu assasa ta’addancin Boko Haram.
Dama dai UN ba ta jin dadin abubuwan da su ke faruwa a halin
yanzu a Najeriya musamman a bangaren sha’anin tsaro da kuma matsin tattalin
arziki. ’Yan ta’addan Boko Haram na amfani da kananan yara wajen samun kudi da
dasa bama-bamai
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> whatsapp://chat?code=41x2TuRqdVQ9PrcrucqpTu Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira
Hausa.naij.ng
Tags:
LABARI