Kotun na zargin Idris da raina umarninta na sakin Mista
Olalekan Alabi, wani mataimaki na musamman a kan harkokin siyasa ga gwamnan
jihar Kwara, Abdulfatah Ahmed.
Barazanbar tura Sufeto Idris gidan yarin na kunshe ne cikin
wata takardar jan kunne mai lamba ta 48 da kotun ta buga a ranar 10 ga watan
Agusta. Takardar da aka raba ga manema labarai yau, Alhamis, a Ilorin ga manema
labarai na dauke da saka hannun rajistaran kotun.
A cikin takardar, a lkalin kotun, Yusuf, ya ce “ka sani
cewar matukar baka yi biyayya ga umarnin babbar kotu dake jihar Kwara ba a kan
hukuncin da ta yanke ranar 1 ga watan Agusta, 2018, ba tamkar nuna raini ga
bangaren shari’a ne wanda hukuncinsa shine tisa keyar ka zuwa gidan yari.”
Hukumar ‘yan sanda ta kama tare da tsare Alabi ne tun ranar
30 ga watan Mayu bayan an yi zarginsa da alaka mai karfi da ‘yan fashin garin
Offa. Sai dai mai shari’a Yusuf ya bayar da umarnin a saki Alabi a kan beli na
wucin gadi a ranar 1 ga watan Agusta tare da bayyana cewar babu hujjar cigaba
da tsare shi.
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> whatsapp://chat?code=41x2TuRqdVQ9PrcrucqpTu Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira