• Labaran yau

  Bidiyon N21b da bindigogi 400 a gidan Lawal Daura ba gaskiya bane, DSS ta karyata

  Wata sanarwa da ta fito daga hedikwatar hukumar DSS na tarayya da ke Abuja ta karyata tare da nisanta kanta daga wasu faya fayin bidiyo da ke zagayawa a kafofin sada zumunta cewa an sami wasu kudade N21b, tare da bindigogi 400 a gidan tsohon shugaban hukumar, Lawal Daura, bayan an kore shi daga mukaminsa ranar 8 ga watan Agusta.

  Sanarwar hakan ta fito ne daga bakin mai magana da yawun hukumar Toni Opuiyo ta wata sanarwa da ya aike wa manema labarai.

  Opuiyo ya ce babu wata hukuma ko DSS da EFCC basu gudanar da bincike da aka sami wadannan ababe da ake alakantawa da lamarin ba, kamar yadda ake nunawa a shafukan sada zumunta da yanar gizo.

  Hakazalika, Opuiyo, ya bukaci jama'a su kaurace wa rura wutar labaran karya, a cewarsa domin shugaban kasa ya sha alwashin kaddamar da cikakken bincike a kan abin da ya faru ranar 8 ga watan Agusta da ya kai ga tura jami'an DSS domin su dakile kofar shiga Majalisar tarayya.  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> whatsapp://chat?code=41x2TuRqdVQ9PrcrucqpTu 
  Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com
  Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Bidiyon N21b da bindigogi 400 a gidan Lawal Daura ba gaskiya bane, DSS ta karyata Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });