• Labaran yau

  Fadar shugaban kasa ta dau zafi, Buhari ya fusata da koran shugaban DSS Lawal Daura

  Bayanai daga birnin Abuja sun nuna cewa akwai yar damuwa a fadar shugaban kasa domin dai shugaba Buhari ya fusata sakamakon yadda aka kori shugaban DSS Lawal Daura daga mukaminsa.

  Ranar 8-8-2018 ne Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya kori Lawal Daura daga mukaminsa bayan wasu matsaloli da suka jibanci yadda jami'an DSS suka dakile kofar shiga Majalisar Wakilai da sanyin safiyar ranar 8 ga watan Agusta.

  Lamari da ya jawo cacan baki tsakanin yan Najeriya  da ma kasashen Duniya da suka yi ta yin Allah wadai da yadda aka gan hotunan jami'an DSS dauke da makamai sun dakile kofar shiga Majalisar Najeriya.

  Politicsngr ce ta ruwaito haka, haka zalika majiyar ta ce duk da yake akwai wasu ababe da suka jibanci katsalandan ga abin da wasu ke gani kamar tsaron kasa, amma ana fargaban cewa ba a sanar da Buhari ba kafin a kori Daura daga mukaminsa.

  Shugaba Buhari dai, ya mika wa mataimakinsa Osinbajo cikakken iko kafin ya bar Najeriya zuwa hutu na kwanaki goma.

  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> whatsapp://chat?code=41x2TuRqdVQ9PrcrucqpTu
  Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com
  Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Fadar shugaban kasa ta dau zafi, Buhari ya fusata da koran shugaban DSS Lawal Daura Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });