Mininstan Sufuri na kasa Rotimi Amaechi ya bayyana cewa
matsalar kudi ce ta kawo tsaiko akan aikin ginin titin jirgin kasa wanda ya
taso daga Ibadan zuwa Kaduna, duk da cewa akwai yarjejeniya da aka rattaba.
Amaechi wanda ya bayyana hakan ga manema labarai a garin
Warri, ya ce aikin za ayi shi ne da bashin da aka karbo daga bankin Exim da ke
China, amma kawo yanzu kudin bai zo ba, wanda hakan ya kawo tsaiko fara aikin.
“Mun sanya hannu a yarjejeniyar da za ta ba mu damar karbo
rancen kudi kimanin sama da Dalar Amurka biliyan $6.7billion, wanda hakan zai
bamu damar fara aikin gina titin jirgin kasan cikin kwanciyar hankali, Amma
Bankin da zai bada wannan makudan kudaden wato Bankin Exim da ke kasar China,
ya bukaci mu rage yawan kudaden" in ji Amaechi
Ya kara da cewa gwamnatinsu ta yi nasarar samar da kudin da
aka yi titin dogo wanda ya tashi daga Itakpe zuwa Warri tare kuma da kammala
aikin titin dogo daga Abuja zuwa Kaduna, wanda ya lashe zunzurutun kudi kimanin
$1billion.
A karshe ya bayyana cewa kimanin mutane 150 aka dauka aiki
bayan kammala aikin titin dogo wanda ya taso daga Abuja zuwa Kaduna, ya kuma ce
wannan ba komai bane domin kuwa da zarar an kammala sauran layukan dogno, to
babu shakka al'ummar kasar nan za su samu karin aikin yi.
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> whatsapp://chat?code=41x2TuRqdVQ9PrcrucqpTu
Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com
Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira
Hausa.naij.ng
Tags:
LABARI