• Labaran yau

  Zaben Ekiti: An cafke wasu mutum 5 suna raba wa jama'a kudi lokacin zabe

  Yansanda sun damke akalla mutum 5 a Ado Ekiti bayan an yi zargin suna raba wa jama'a kudi lokacin zaben Gwamnan jihar Ekiti da ake yi ranar Asabar. An damke wadannan mutane ne a gaban wata Mazaba da ke makarantar Jonathan Memorial a unguwar Ajilosun na babban birnin jihar ta Ekiti. 

  Tun farko dai wasu yan takarar kujerar gwamna a karkashin jam'iyyun Mega party da Accord party watau  Bisi Omoyeni da Abiodun Aluko, sun yi zargin cewa wasu jama'a na ba masu kada kuri'a kudi domin a sayi kuri'unsu.

  Dan takarar kujerar Gwamna a karkashin jam'iyar Accord party Abiodun Aluko, ya yi zargin cewa jam'iyar APC tana ba masu kada kuri'a N5000 a bayyane, domin su kada ma dan takarar APC kuri'a, ya ce ita kuma PDP tana ba jama'a N4000, bayan N3000 da ta biya a asusun ajiya na ma'aikatan gwamnatin jihar Ekiti.
   
  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/Lq4Z5kPck53Le3ibU9RUnY Latsa nan domin ka sauke Manhajarmu ISYAKU.APK https://docs.google.com/uc?export=download&id=0B7lmLLhGZSx5OTVENFlsTkllRTQ Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Zaben Ekiti: An cafke wasu mutum 5 suna raba wa jama'a kudi lokacin zabe Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama