Ciwon zuciya ko bugun zuciya har yanzu shine na daya da yan Nijeriya
suke fama dashi, inda hakan ya nuna cewar, a duk cikin mutane goma, uku
na fama da ciwon.
Alamomin sun hada da, jin zafi a kirji da yawan yin zifa da jin
kasala da wasu sauran alamau da za ku gansu a bayyana kamar yadda
likitoci suka bayyana.
1. Kasala: Jin kasala tana daya daga cikin alamomin bugun zuciya
musamman ga mata. Mutanen da zasu fara kamuwa da bugun zuciya zasu fara
jin kasala kuma zasu ji sun kasa yin wani aiki. Aceawar kafar WebMD,
hakan ya sanaya a lokacin bugun zuciya jinin dake zagayawa a zuciya yana
raguwa da kuma sanya jin gajiya a damtse. Don ka kare lafiyar ka ya
zama wajibi kaje kaga likita ba tare da bata wani lokacin ba don ya duba
lafiyar ka.
2. Raguwa yin numfashi; Zaka dinga jin raguwar numfashin ka, alala
misalai idan ka hau bene zaka dinga yin haki. In har kaji kana yin
numfashi da kyar da jin gajiya bayan ka yi yar tafiya to wanana alamu ne
na ka kamu da bugun zuciya. A cewar MayoClinic, zuciya tana taka rawa
sosai wajen tura iska zuwa sassan jikin dan adam da kuma cirewa wasu
sanadaran da jikin baya bukata.
3. Jin zafi mai radadi a zuciya: Idan kana jin zafi mai radadi a
zuciya wanda kuma bai cika damun ka ba, ka tabbatar da ka tuntubi
likitan ka domin wannaa alamu ne na bugun zuciya kumawannan alamar tana
hana jinni yawo zuwa zuciya.
4. Gurbacewar ciki: Bugun zuciya wani lokacin yakan janyo lala cewar
ciki kamar jin amai,inda hakan ya kan faru ne saboda wani irin abinci da
kaci.
5. Fesowar kuraje a baya ko a damtsen hannu ko a cikin kirji: Jin
zafi a wadanan wurare alamomi ne na an kamu da bugun zuciya kuma hakan
yana janyo rashin fitar iska saboda jijiyon jinni sun rufe. Idan ka fara
jin alamu ka tabbatar da kaje kaga likita.
6. Jin rashin sukuni a makogoro ko wuya ko a mukamuki: A nan zaka
dinga jin rashin sukuni a makogwaraon ka ko a wuya ko kuma a mukamukin
ka wanda kuma baka taba jin irin sa a baya ba, haka mutane m,asu fama da
ciwon siga, sukan mayar da hankali a dukkan wani chanji da suka ji a
jikin su.
7. Jin wani chanji gaba daya na ba dai dai ba a jiki: A ko da yaushe
ka dinga sauraron wata murya da zaga dinga ji a cikin kanka, wananna ana
yi maka gargadi ne. Wasu marasa lafiya su kan gayawa wasu likitocin su
cewar basa ji sosai a saboda haka ya kamata ka tuntubi likita in ka fara
jin hakan
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/Lq4Z5kPck53Le3ibU9RUnY
Latsa nan domin ka sauke Manhajarmu ISYAKU.APK
https://docs.google.com/uc?export=download&id=0B7lmLLhGZSx5OTVENFlsTkllRTQ
Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com
Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira
al'ummata