Sautin muryar P.A na babban jami'in gwamnatin Bagudu da ya nemi koran isyaku.com daga Kebbi

Isyaku Garba | 13-7-2018 |


Dangane da labari da muka wallafa na yaadda wani babban jami'in gwamnatin jihar Kebbi ya umarci mai taimaka masa watau P.A cewa ya gaya wa isyaku.com ya kwahe kayansa ya bar jihar Kebbi kafin su dawo daga Abuja ranar Juma'a 29-6-2018. Wasu bayanai sun biyo baya sakamako yadda aka tswala karya domin a bata suna isyaku.com bisa yanaiy na cin amana da nuna danniya ta hanyar nuna rashin tausayi daga wadanda zuciyarsu ta bushe suka bige cikin barsar mulkin Allah ya isa.

Wata majiya ta tabbatar mana cewa shi wannan jami'in gwamnati ya ce gidan gwamnatin jihar Kebbi ta sha tallafa wa isyaku.com domin ya inganta shafinsa ganin yadda isyaku.com ke bayar da labarai na jihar Kebbi musamman kasancewa kafa sa'idiya wacce ke tsaga gaskiyar labarai musamman na jihar Kebbi ba tarae da nuna banbanci ba.

Bisa wannan karya da aka shata wa isyaku.com, mawallafin shafin ya tabbatar da cewa karyace zunzurutu daga bakin wanda baya jin kunyar shata karya, a tunaninsa, karya wata salo ce ta samun biyan bukata a harkar Siyasa. Anan, isyaku.com ya tsaya a bakan sa cewa babu ko sisin gwamnatin jihar Kebbi a wajen tafiyar da shafin isyaku.com, idan kuma akwai wani tallafi ko taimako da aka taba bayarwa daga gidan gwamnati domin a ba isyaku.com, tau gwamnatin jihar Kebbi ta sani cewa ba wanda ya taba ba isyaku.com ko sisi da sunan gwamnati.

Wannan ya sa na tuna da hira da Mujallar isyaku.com ta yi da Hon. Yakubu Bello Rilisco inda ya ce "Ba abin da ke saurin cin dan siyasa da wuri kamar yin karya" .

Bayan karya da aka yi na taimaka wa isyaku.com, haka zalika an karyata labarinmu domin cewa aka yi ai wasa ne ake yi ba wai da gaske akace a gaya wa isyaku.com ba. Amma idan mai magana wawa ne ai mai sauraro ba wawa bane. Domin jama a su yi hukunci ga, sautin yadda tattaunawar mu ta kasance tsakanin isyaku.com da mai taimaka wa babban jami'in gwanmati jihar Kebbi:

Latsa nan ka sauke sautin: Download = Umarnin cewa isyaku.com ya kwashe kayansa ya bar jihar Kebbi

Ya zama wajibi mu fara sakin hujjoji ganin yadda wannan bawan Allah ya ci amanar mu, muka yi hakuri muka barshi da Allah muka tafi salin alin ba tare da kowa ya ji ba, amma ya ci gaba da cin zarafin mu har da cewa shi bai gan aikin da isyaku.com ya yi masa ba da zai biya shi hakkin shi.

Mun dai nuna da'a, biyayya tare da hakuri domin mutunci, ragowa bin na gaba tarbiyyar ginan mu ce. Amma isyaku.com ya jawo Alh. Sani Dododo cikin takaddamar. Duk da haka wanna taliki ya yi biris da hakkin mu wanda bayan N400.000 da isyaku.com ke binsa, har da N200.000 na rubutun gyara barnar labarin jarida da ake kira REJOINDER, wanda muka wallafa masa a kebbi24.com. Sai kuma tallar motoci da yake yi ma kwaskwarima wanda har muka jawo wasu Mujalloli masu zaman kansu na wasu jihohi a arewacin Najeriya, ya kamata ya bamu N200.000 amma ko sisi bai bayar ba, ya hada mu fada da sauran 'yan uwanmu mawallafa wasu shafuka, mun sa mashi ido bamu ce komi ba.


Domin tabbatar da rashin godiya da nuna danniya wannan talikin ya kirgo wasu 'yan labari da basu wuce 39 ba cewa su ne kadai isyaku.com ya wallafa masa a cikin wata 6 na zaman kwangila da ya yi tare da shi wanda aka gina bisa yarda, amana da mutunci. Muna da hujjoji a kan wannan. Ai ko makiyin jihar Kebbi ya san mun yi aiki tsakani da Allah. Idan har labari 39 ne kadai muka wallafa a cikin fiye da wata 6, ai duk inda ya tafi muna tare da shi ko?, za mu kira wannan cewa an bata mana lokaci kenan ganin cewa an wulakantar da lokacinmu har tsawon wata 6 kenan ? wannan talikin baya da dukiya da zai iya biyanmu lokaci da ya bata mana na tsawon wata 6 !.

Bai kuskure ne babba rayuwa kowa ya shaide ka da rashin godiya ko yabawa duk wani aikin kirki da aka yi maka, bai da kyau a shaide ka da karewa da cin mutunci da rashin nuna dattaku a kowane al'amari da aka fara shi cikin mutunci da kai, daga karshe sai ka wulakanta mutane wai kai mai mulki a jihar Kebbi daga 2015 zuwa 2019. Haka zalika ba daidai bane ka yi tunanin cewa kowa dabba ne tunda kana kan wani matsayi na aro, tsananinta idan ka bi guguwar siyar darajar dan Bagudu aka sake cin zabe ka sake maimata wasu shekara 4 waanda bayansu ko Alade zai fi ka daraja a ciki al'umma matukar baka gyara ba wajen neman shiri da mutunta jama'a da ka dauke su kamar bayi ba tarae da kula da jin dadin rayuwarsu ba duk da yake dan Bagudu na bayar da wadannan alawus.

Mai girma Gwamnan jihar Kebbi Sanata Atiku Abubakar Bagudu ya taba kiran isyaku.com ta wayar salula a cikin watan Oktoba na 2017, ya nuna jin dadi yadda isyaku.com ya kirkiro wannan shafuka masu zaman kansu na isyaku.com da kuma kebbi24.com, Gwamna Bagudu ya ce "Ina shaida maka cewa duk abin da kake yi a yanar gizo muna gani, kuma a madadin ni kaina da 'yan Majalisa ta ta jihar Kebbi da Majalisar zartarwa ta, ina yi maka godiya sakamakon wannan abin da ka yi. Nan gaba idan Allah ya yarda, zan kira ka ka zo nan gidan Gwamnati domin akwai abin da ya kamata ka yi mana".

Wadannan kalamai ne da isyaku.com ba zai manta da su ba har abada, domin an mutunta mu, an darajantamu, an karrama mu duk da yake har yanzu Gwamnan bai kira mu ba balle mu bayar da tamu gudunmuwa. Amma kuma bamu gan laifin gwamnati ba domin shafin mu ba don gwamnati muka yi ba, kudin mu muka sa muka yi tare da basirar mu, domin daukaka daraja da mutuncin jama'ar jihar Kebbi. Isyaku.com da kebbi24.com ne kadai shafuka masu zaman kansu a tarihin jihar Kebbi, amma ka tambayi Google "Kebbi state" sai ka duba Wikipedia ko ka tambayi Google "isyaku.com" domin ka tabbatar da wanzuwar aikin mu na girka sunan jihar Kebbi bisa alhairi a Duniya ba wai a batanci ba.

Mun sa ido mu gan yadda al'amurra ke tafiya, kuma muna kira ga duk dan asalin jihar Kebbi a ko ina yake a fadin Duniya cewa idan ya aiko mana da labari kyauta za mu wallafa labarin idan ba na kasuwanci, siyasa ko cin zarafin wani bane. Ko da turanci ko Hausa watau a kebbi24.com ko a isyaku.com.

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/Lq4Z5kPck53Le3ibU9RUnY Latsa nan domin ka sauke Manhajarmu ISYAKU.APK https://docs.google.com/uc?export=download&id=0B7lmLLhGZSx5OTVENFlsTkllRTQ Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN