Yaro ya yanke al'aurar safeton dansanda sakamakon yunkurin aikata luwadi da shi

Wani safeton dansanda (mun sakaya sunansa) ya rasa al'aurarsa bayan wani yaro dan shekara 13 ya yanke al'urar safeto da wuka yayin da yake yunkurin aikata ludu da shi a unguwar Tudun Markabu da ke karamar hukumar Faskari a jihar Katsina.

Wata majiya da bata son a ambaci suna , ta ce wannan safeton dansanda dabi'ar shi ce ta aikata wannan aiki da yara a cikin unguwar, ya kuma ce, yaro na karshe fa amfani ya yi da wuka ya yanke al'aurar wannan safeto.

Bayanai sun tabbatar cewa yaran sun dana ma safeto tarkone kuma  ya fada, bayan ya addabe su da yawan aikata wannan aiki.

Vanguard ta ruwaito cewa an canja ma safeto wurin aiki ne daga karamar hukumar Sabuwa zuwa Kankara, kafin a tura shi aiki a Faskari in da dubu ta cika, yaro ya yanke masa al'aura ranar Talata da dare.


Kakakin yansanda na jihar Katsina Gambo Isah ya tabbatar da faruwar lamarin. Ya ce " mun sami labarin wannan abin kunya, bamu tsammanin jami'an mu su kasance masu aikata irin wannan aiki".

Safeto dai yana babban Asibitin Faskari kuma an tura shi zuwa babban Asibitin Katsina, amma yana a Faskari.

Gambo ya kara da cewa " rundunar mu tana bincike a kan lamarin, kuma idan ya warke za mu tara shaidu, idan aka same shi da laifi, za mu gurfanar da shi a gaban Kotu".

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/Lq4Z5kPck53Le3ibU9RUnY Latsa nan domin ka sauke Manhajarmu ISYAKU.APK https://docs.google.com/uc?export=download&id=0B7lmLLhGZSx5OTVENFlsTkllRTQ Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN