Kebbi: Yansanda sun kama bafulace da ya kashe wani safeton dansanda a Bagudo

isyaku.com | 12-7-2018

Rahotanni daga garin Ka'oje na jihar Kebbi na cewa  wani bafulace ya kashe wani safeton dansanda ranar Laraba 9 ga watan Juli.

Dansandan ya je garin Bagudo ne domin ya gayyato bafulacen bayan wani manomi ya yi kararsa cewa ya shiga gonarsa da shanaye kuma sun yi mashi barna ga amfanin gonarsa.

Bayan an shigar da karar ne sai aka tura safeton domin ya taho da bafulacen, yayin da ya kamo bafulacen a kan hanyarsu ta zuwa wajen motar sintiri na yansanda, sai bafulace ya zare adda ya caka ma safeto a wuya. Sakamakon haka jini ya yi ta zuba, lamari da ya haddasa mutuwar safeto.

Kakakin yansandan jihar Kebbi DSP Mustapha Suleiman, ya tabbatar da faruwar lamarin, ya kuma ce yansanda sun kama bafulacen wanda tuni ya amsa laifin aikata kisa.

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/Lq4Z5kPck53Le3ibU9RUnY Latsa nan domin ka sauke Manhajarmu ISYAKU.APK https://docs.google.com/uc?export=download&id=0B7lmLLhGZSx5OTVENFlsTkllRTQ Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN