"Yansanda sun waska mini mari, sun harbeni, ina fama da ciwo" Fayose

Gwamna Ayodele Fayo na jihar Ekiti, ya shaida wa 'yan rahoton gidan Talabijin na kasa da Channels Tv cewa "jiki na na ciwo ko ina, kuma yansanda sun harbe ni". Gwamnan ya kara da cewa "ba zan jure wannan ba ko kadan" daga bisani Gwamnan ya kauce wa Kamera yayin da hawaye ke fitowa daga idanunsa.

Wannan ya faru ne 'yan mintoci bayan Gwamnan ya bayyana sanye da neck brace ya da bandeji a hannunsa na hagu, yi jawabi a wajen taron gangamin jam'iyar PDP ranar Laraba, kafin zaben da ake shirin yi na Gwamna a jihar Ekiti ranar Talata.

Fayose ya shaida wa jama'a da suka taru awajen gangamin cewa "ina shaida wa Duniya cewa jihar Ekiti na cikin tsaka mai wuya. Ta yaya zan kasance Gwamna a cikin jihata kuma a yi mini irin wannan abu a cikin kasata?. Jama'ata, ina kira gareku ku tsaya bisa kafafuwanku.Zan koma Asibiti domin in huta, ina jin tsananin ciwo a jiki na, amma na gommace in dau wannan ciwo saboda ku".

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/Lq4Z5kPck53Le3ibU9RUnY Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN