Yansandan jihar Kebbi sun kama mutum 11 masu satar mutane da shugaban barayin motoci

Isyaku Garba | Birnin kebbi | 25-7-2018 |


Rundunar Yansandan jihar Kebbi ta kama mutum 11 masu satar mutane tare da shugaban wani gungun masu satar motoci a fadin jihar. Kwamishinan yansandar jihar Kebbi Ibrahim Kabiru ya shaida wa manema labarai haka a Birnin kebbi ranar Talata.

Kabiru ya kara da cewa " Rundumnarmu ta kama wasu gungun masu satar babura a jihar Kebbi tare da shugaban gungun mai suna Zaki Mamman.

Haka zalika mun kama wasu yan kungiyar masu satar motoci a cikin jihar Kebbi tare da shugabansu mai suna Mr. Peter James, kuma za mu gurfanar da su a gaban Kotu.


Rundunarmu ta bullu da wasu sababbin matakai domin ganin mun fuskanci sababbin salon aikata laifi da bata gari suka bullo da shi a fadin jihar Kebbi."

Kwamishinan ya ci gaba da cewa " Rundunar mu ta gurfanar da mutum 224 daga cikin mutum 291 da ta kama wanda daga cikin adadin an yanke wa mutum 201 hukunci yayin da mutum 17 ke jiran shari'a".

Ya kuma bukaci al'ummar jihar Kebbi su kasance masu kula tare da yin taka tsantsan da kasuwanci da ake gudanarwa ta yanar gizo duba da cewa ana yawan samun matsala ta yaudara ko cuta a wasu lokuta. Ya roki jama'a su dinga taimaka wa yansanda da bayanai da zasu kai ga cafke bata gari a cikin al'umma.

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> whatsapp://chat?code=41x2TuRqdVQ9PrcrucqpTu Latsa nan domin ka sauke Manhajarmu ISYAKU.APK https://docs.google.com/uc?export=download&id=0B7lmLLhGZSx5OTVENFlsTkllRTQ Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN