Sani Musa Saminaka | Shanga | 24-7-2018 |
Da sanyin safiyar Talata a garin Saminaka na karamar hukumar Shanga a jihar Kebbi, wani saurayi ya dalla ma Mahaifiyarsa mari har sau uku masu karfin gaske sakamakon tsananin fusata da ya yi da ita.
Wakilinmu ya shaida mana cewa lamarin ya samo asali ne tun daren Litinin, bayan saurayin ya sami matsala da wata kaunarsa bisa zargin cewa ta saba masa, sakamakon haka ya lafta mata na jaki har lamarin ya wuce misali.
Majiyar tamu ta ce sakamakon haka ne fa Mahaifiyarsa ta dauki mataki, domin ganin irin wannan hukunci nasa a kan kaunarsa bai sake faruwaba domin gudun tsautsayi wata rana.
Ana cikin haka ne sai wata sabuwa ta sake bullowa da sanyin safiyar Talata, domin dai ganin aka yi wannan saurayi ya sake maimaita waccan duka wa kaunarsa da aka hana shi tun daren Litini, ganin haka ke da wuya sai Mahaifiyarsa ta yi wuf ta shiga tsakani domin ta hana shi ci gaba da lafta wa kaunarsa na jaki, amma sai gogan naka ya kalli Mahaifiyarsa ya dalla mata mari har sau uku.
Majiyarmu ta tabbatar manaa da cewa, ganin haka ke da wuya, su ma yanuwansa da magabatansa suka kama shi suka lafta masa na jaki watau ya sha dan karen duka, ya daku da kyau domin ya zama darasi da izna gareshi da duk wani mai tunani irin nasa a cikin dangi.