NDLEA a jihar Kebbi ta kama boka mai gonar wiwi a karamar hukumar Fakai

Rundunar hana sha da tu'ammali da miyagun kwayoyi na jihar Kebbi NDLEA, ta kama wani Mai maganin gargajiya mai suna Arage Rikici dan shekara 55 wanda ya mallaki wata gonar tabar Wiwi a kauyen Kukin na karamar hukumar Fakai.

Kwamandan rundunar ta jihar KebbiSuleiman Jadi, ya shaida wa wakilin kamfanin dillancin labarai na Najeriya haka yayin zantawa da shi a Birnin kebbi.

Ya ce bisa wani labari na sirri da rundunarsa ta samu ne, jami'ansa suka yi dirar miliya a gonar kuma daga bisani suka lalata Wiwi da aka shuka, yayin da aka damke mai gonar Arage Rikici kuma aka kai shi babban ofishin hukumar da ke Birnin kebbi inda yake fuskantar bincike.

Arage ya ce "ina da gonar tabar wiwi a gonata wadda take kusa da gidana, kuma ina biyan yara kudi domin su taya ni nomansa,  na samo irin wiwin daga kasar Jamhuriyar Benin. Kuma ina sayar da kulli daya a kan N50 ga masu amfani da shi".


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> whatsapp://chat?code=41x2TuRqdVQ9PrcrucqpTu Latsa nan domin ka sauke Manhajarmu ISYAKU.APK https://docs.google.com/uc?export=download&id=0B7lmLLhGZSx5OTVENFlsTkllRTQ Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN