Sharri kare ne,idan ya kai sako zai dawo maka, Fayose 2014, Fayose 2018

Isyaku Garba | 11-7-2018 |

Sakamakon yadda lamurra suka cakude wa Gwamna Fayose a siyasar jihar Ekiti a yau Laraba bayan Gwamnan ya suma har sau biyu sakamakon barkonon tsohuwa da yansanda suka harba a kusa da gidan Gwamnatin jihar Ekiti ,bayanai sun bulla cewa amana ce ta kama shi.

Hausawa sun ce sharri Kare ne, idan ka aike shi, zai dawo wajenka. A shekara ta 2014, lokacin zaben Gwamnan jihar Ekiti, ana zargin cewa shugaban kasa na waccan lokaci Goodluck Jonathan ya umarci shugaban askarawan sojin Najeriya na wancan zamani CDS Alex Badeh, inda ya yi amfani da sojoji suka ci zarafin karamin Ministan tsaro Musliu Obanikoro tare da tawagarsa, wanda suka je jihar Ekiti domin sa ido a kan yadda zaben Gwamna zai kasance.

A yau kuma , reshe ya juya da Mujiya, sai ga Gwamna zaune a doron kasar Allah ya suma, ana zuba mashi piya wata kafin ya farfado.

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/Lq4Z5kPck53Le3ibU9RUnY Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN