‘Yan sandan tawagar Osinbajo sun zane jami’an kwastam a Katsina


A jiya ne jami’an ‘yan sandan tawagar mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, sun zane wasu jami’an kwastam uku a Katsina

Lamarin ya faru ne a kauyen Daddara na karamar hukumar Jibia ta jihar Katsina inda Osinbajo ya kai ziyara domin jajantawa jama’ar da iftila’in ambaliyar ruwa ta yiwa ta’adi tare da salwantar rayukan mutane fiye da 50. An samu hatsaniya ne bayan jami’an kwastam sun tsare motar wasu matasa dake dauke da haramtattun kaya da ta fito daga jamhuriyar Nijar.

A yayinda jami’an kwastam din suka tsare motar ne tawagar shugaban kasa ta zo wucewa ta kauyen na Daddara. Wani shaidar gani da ido ya bayyana cewar jami’an kwastam din na kokarin matasan da suka taru a wurin ne amma sai jami’an ‘yan sanda dake tawagar Osinbajo suka yi kuskuren daukan hakan a matsayin wata barazana ga tawagar mataimakin shugaban kasar, saboda jami’an na kwastam na amfani da bindigu domin tarwatsa matasan dake kokarin fin karfinsu domin kwace motar da suka kama.

“Nan da nan ‘yan sandan tawagar mataimakin shugaban kasa suka diro daga motocinsu tare da kokarin kwace bindigogin dake hannun jami’an na kwastan. Bayan kwastam din sun ki basu bindigun ne sai suka fara marinsu da dukansu,” a cewar shaidar. Shaidar ya kara da cewar, “ganin ana dukan jami’an kwastam din ne sai matasan da suka taru su ma suka fara jifansu da duwatsu. Tuni matasan da aka kama motar su suka arce kafin a gama hayaniyar.”
 


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/Lq4Z5kPck53Le3ibU9RUnY Latsa nan domin ka sauke Manhajarmu ISYAKU.APK https://docs.google.com/uc?export=download&id=0B7lmLLhGZSx5OTVENFlsTkllRTQ Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira

Hausa.naij.ng
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN