• Labaran yau


  Makiyaya sun damke barayin shanayensu yayinda suka kawo kasuwa sayarwa, sun kashe su nan take


  Makiyaya sun kashe wasu barayin shanu guda shida a yayin da suka kai shanu kasuwar Iware dake Ardo-kola a jihar Taraba domin sayarwa.

  Rundunar yan sanda ta shaidawa manema labarai faruwar lamarin, inda suka ce barayin sun kai shanun kasuwar yankin Lai wanda a nan ake rikicin Fulani da Makiyaya domin su sayar da su, amma su kayi rashin sa'a Fulanin suka gane shanunsu, abinda ya kai ga har barayin sun rasa rayukansu.

  Kakakin hukumar yan sanda ta jihar ASP David Misal, ya tabbatar da afkuwar lamarin. Misal ya ce "Ya zuwa yanzu bamu samu cikakken bayani akan wadnda aka kashen ba, sannan ba zamu iya tabbatar ko daga yankin Lau suke ba". "Muna cigaba da bincike domin gano wanda suka dauki doka a hannunsu maimakon su kawo wa hukuma domin yin bincike".
   

  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/Lq4Z5kPck53Le3ibU9RUnY Latsa nan domin ka sauke Manhajarmu ISYAKU.APK https://docs.google.com/uc?export=download&id=0B7lmLLhGZSx5OTVENFlsTkllRTQ Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira

  Hausa.naij.ng
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Makiyaya sun damke barayin shanayensu yayinda suka kawo kasuwa sayarwa, sun kashe su nan take Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama