Abubakar Kori dan shekara 25, wani wada ne dan Boko Haram da ke amfana da N5000 a duk lokacin da ya taimaka aka kai harin bam a birnin Maiduguri da kewaye.
Abubakar yana cikin yan Boko Haram 22 da rundunar yansanda ta kama a jihar Borno da Yobe a ci gaba da farautar yayan kungiyar da take yi.
Ya kuma ce shi mai gadi ne a wani gidan Mai a garin Dolari, kuma ya sha taimakawa domin a kai harin bam. Wani sa'ilin ma tare da she ake zuwa wajen danawa da tayar da bam din, daga bisani yake samun N5000 daga wani mai suna Ba'adam wanda ya ce yana daya daga cikin Madugun shirin kai hare haren bam a Maiduguri da kewaye.