Wasu samari guda biyu da suka mayar da kansu barayin awaki karfi da yaji sun fada tsaka mai wuya, bayan asirin su ya tunu yayin da suka saci wata uwar Akuya a kauyen Eziagulu da ke garin Nnewi a jihar Anambra daga gidan wata mata mai suna Mrs. Roseline.
Bayan barayin Ifedichukwu
Iloduba da Chika Umeakunne sun yi nassarar satar Akuyar a karo na farko, sai ja'iran suka sake komawa ranar Talata domin su saci sauran kananan diyan Akuyar, nan fa asiri ya tonu.
Wadannan barayi dai sun sha dukar tsiya, kuma aka zagaya da su a cikin gari domin jama'a su gansu.