Mun samu rahoton cewa hukumar 'yan sanda reshen jihar Ondo
ta dakume wani gawurtaccen dan fashi da ya yi kaurin suna tare da shahara akn
satar Motoci. A yayin gabatar da wannan dan ta'adda, Olayemi Adeoye ga manema
labarai a shelkwatar hukumar dake birnin Akure, kakakin ta Femi Joseph ya
bayyana cewa, azal ce ta afka ma sa yayin da yayi yunkurin satar wata mota
kirar Toyota Corolla mallakin wani mutum, Mista Olanipekun. Hukumar ta dakume
Olayemi tare da abokin sana'ar sa, Waheed Anifowose, mai facin taya da ya saba
kawo masu sayen motocin da zarar an sato su.
Olayemi mai sana'ar Walda da hukumar 'yan sanda ta dakume
yayin satar motar mai lamba SS719 AAA ya bayyana cewa, ya na matukar samun
annashuwa da farin ciki a duk sa'ilin da yayi satar mota musamman masu amfani da
dan mabudi. Kakakin ya ci gaba da cewa, Olayemi ya shiga hannun hukumar ne inda
aka sallame shi a ranar 15 ga watan Yunin da ya gabata kafin ta sake kai masa
wawura a wannan lokaci.
Mista Femi ya kara da cewa, akwai sa hannun Olayemi a satar
Motoci 32 cikin shekarun biyun da suka gabata, sai dai yana mamakin yadda yake
kubuta daga dauri kuma ya sake komawa cikin al'umma inda yake ci gaba ta tafka
ta'asar sa .
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> whatsapp://chat?code=41x2TuRqdVQ9PrcrucqpTu Latsa nan domin ka sauke Manhajarmu ISYAKU.APK https://docs.google.com/uc?export=download&id=0B7lmLLhGZSx5OTVENFlsTkllRTQ Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira
Hausa.naij.ng