Wani Jirgin sama mai saukar ungulu ya sauka a sabon gidan
gwamnati, Ayoba Villa, Ado Ekiti, babban birnin jihar Ekiti.
Jirgin ya sauka ne a gidan gwamnatin jihar da ranan nan. Ana
zargin cewa jirgin mai saukar ungulu ya kawo kudade ne gana wani gwamnan Kudu
maso kudu. Mambobin jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP) na ta zarya a
gidan gwamnatin don karban kudi. Suna ta shiga gidan gwamnati ta karamin kofar
tsohon ofishin gwamnan
An gano wata mace yar jam’iyyar dake korafin cewa ba’a bata
nata kason daga kudin ba.
Ta ce: “Ba’a bani nawa kason ba alhalin wasu sun karba sau
biyu ko. “Duk wanda ya karbi kudin nan sannan ya ki zabar Eleka ba zai rayu har
ya kashe kudin da hannunsa ba.”
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/Lq4Z5kPck53Le3ibU9RUnY
Latsa nan domin ka sauke Manhajarmu ISYAKU.APK
https://docs.google.com/uc?export=download&id=0B7lmLLhGZSx5OTVENFlsTkllRTQ
Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com
Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira
Hausa.naija.ng