Wata bangare na jam'iyyar APC a jihar Kaduna dake yiwa kanta
lakabi da APC Akida dake mambobin kungiyar APC Restoration sun sanar da
ficewarsu daga jam'iyyar ta APC baki daya.
Premium Times ta ruwaito cewa kungiyar tace sun yake
shawarar ficewa daga APC ne saboda jam'iyyar ta gaza cika alkawurran data dauka
wa miliyoyin 'yan Najeriya da suka jefa mata kuri'a. Kungiyoyin biyu sun bayar
da sanarwar ficewarsu ne a wata taron manema labarai da suka kira a garin
Kaduna kakashin jagorancin shugaban APC Akida, Mataimaki Maiyashi da Ja'afaru
Ibrahim shugaban APC Restoration. Kungiyoyin biyu basu bayyana jam'iyyar da
zasu koma ba amma sunce suna tattaunawa da wasu jam'iyyoyi da suke ganin
akidunsu yazo daya.
A cewar Maiyaki, sun gamsu cewa ficewarsu daga APC shine
abinda yafi dacewa saboda jam'iyyar bata daukan gyra idan an bayyana mata
kurakurenta. Mr Maiyashi yace sun cinma matsayar kiran taron manema labaran ne
bayan tattaunawa da naziri da su kayi da mambobinsu a jihar da ma kasa baki daya.
Sanata Shehu Sani mai wakiltan yankin Kaduna ta tsakiya mamba ne da APC Akida
kuma ya sha yin barazanar ficewa daga jam'iyyar APC amma bai halarci taron
manema labaran ba.
Shugaban ma'aikata na shugaban majalisa Bukola Sarakim
Hakeem Baba-Ahmed wanda shima dan APC Akida ne ya fice daga jam'iyyar ta APC
kwanakin baya .
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/Lq4Z5kPck53Le3ibU9RUnY
Latsa nan domin ka sauke Manhajarmu ISYAKU.APK
https://docs.google.com/uc?export=download&id=0B7lmLLhGZSx5OTVENFlsTkllRTQ
Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com
Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira
Hausa.naija.ng