Suruki ya kashe surukarsa, matasa sun kashe surukin a kauyen Mahuta jihar kebbi

Wani mutum mai suna Tambaya Manu ya kashe surukarsa a kauyen Bangu a garin Mahuta da ke karamar hukumar Fakai bayan ya sareta da adda, sakamakon haka kuma jama'a suka yi masa dukan fitar rai har ya mutu ranar Talata.

Kampanin dillancin labarai na Najeriya NAN ta ruwaito cewa, Tambaya ya sami matsala da matarsa kimanin wata daya da ta gabata, sakamakon haka ya je gidan surukansa domin ya lallashi matarsa ta koma su ci gaba da zaman aure.

Wata majiya ta ci gaba da cewa Surukarsa, watau mahaifiyar matarsa bata aminta da haka ba, daga bisani sai Tambaya ya yi kokarin shiga gidan surakansa domin ya tafi da matarsa da karfi, amma sai surukarsa ta ki yarda, sakamakon haka ya zare adda ya sareta kuma ta mutu nan take.

Ganin abin da ya aikata sai ya yi kokarin tsarewa, amma jama'a suka ci karfinshi kuma suka lakada masa dukan ajali har ya mutu karfi da yaji.

NAN ta ce, kakakin hukumar yansanda na jihar Kebbi DSP Suleiman Mustapha ya tabbatar da faruwar lamarin ,ya ce amma ko da jami'an yansanda suka je kauyen an tarar kowa ya gudu, ya kara da cewa an sami gawar mutum biyu, watau gawar Suruka da Suruki.

Daga Isyaku Garba


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/Lq4Z5kPck53Le3ibU9RUnY Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN