Wata babbar Kotu a garin Ilaro na jihar Ogun, ta yanke ma wani jami'in dansanda mai suna kofur Moruf Awoleke , mai lambar dansanda 389719 hukuncin kisa bayan ta kama shi da laifin kashe wani dan'acaba mai suna Akanji Ahmed.
A 2016 ne dan acaban ya gamu da ajalinsa a hannun wannan dansanda, bayan wata gajeruwar gardama sakamakon kamashi a kan babur bayan karfe 9 na dare, sakamakon wani umarni da kwamishinan yansanda ya bayar a wancan lokaci na hana yin acaba bayan karfe 9 na dare.
Amma bayan yansandan sun yi kokarin wucewa da babur ne, sai cacan bakin ya zafafa da ya sa kofur Moruf ya harbe Akanji.Sakamakon haka ya mutu.
Wannan lamari ya faru a garin Ilaro hedikwatar karamar hukumar Yewa ta kudu a jihar Ogun.
Alkalin Kotun ya zartar da hukuncin kisa ne, bayan ya ce Kotu ta gamsu da hujjoji da masu gabatar da kara suka shigar, wanda a cewarsa, hujjoji ne da ke fayyace a kowani mataki.
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/Lq4Z5kPck53Le3ibU9RUnY Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira