Abin mamaki, wani karamin yaro ya rataye kanshi har ya mutu

An gano gawar wani dan karamin yaro tana lilo cikin wani kangon gida a garin Adiabo na jihar Cross Rivers ranar Litinin. Makwabta ne suka gano wannan gawar a wani yanayi da yayi kama da daukar rai da kansa ta hanyar kashe kanshi.

Amma fa wannan yaro ne karami, babu wanda ya san yadda lamarin mutuwar wannan yaro ta kasance kafin mutuwarsa, amma fa akwai zargin cewa watakila wani ne ya kashe wannan yaro sai ya rataye shi domin a yi tunanin cewa yaron ne ya kashe kanshi.

Yanzu dai hukumomi sun fara bincike akan musabbabin mutuwar wannan karamin yaro a yanayi da ya yi kama da kisan kai da kai ta hanyar rataya.

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/Lq4Z5kPck53Le3ibU9RUnY Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN