Shugaba Buhari ya ƙi amincewa da wasu dokoki 4 na Majalisar Tarayya



Kamar yadda shafin jaridar The Punch ya ruwaito, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya hau kujerar naƙi kan wasu sabbin dokoki hudu da majalisar dokoki ta tarayya ta nemi sahalewar sa tun a ranar 21 ga watan Yunin da ya gabata.

Cikin wata rubutacciyar wasika da shugaban kasar ya aikawa Majalisar ta dattawa inda shugabanta, Dakta Bukola Saraki ya gabatar yayin zaman majalisar da aka gudanar a ranar yau ta Talata.

NAIJ.com ta fahimci cewa, sabbin dokokin hudu da majalisar ta nemi sahalewar shugaban kasa sun hadar da ta; kafa cibiyar bayar da kariya ga yara, kayyade da tabbatar da tarar kowane nau'i na laifi, sanya tara kan kowace ma'aikata ko cibiya da ta aikata laifin kisan kai da kuma wata doka kan bayar da bashi ga harkokin noma.

Rahotanni sun bayyana cewa, shugaban kasa Buhari ya bayyana dalilan sa filla-filla dangane da rashin amincewa da wannan sabbin dokoki da majalisar ta dattawa ta nemi sahalewar sa tun a ranar 21 ga watan Yunin da ya gabata.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/Lq4Z5kPck53Le3ibU9RUnY Latsa nan domin ka sauke Manhajarmu ISYAKU.APK https://docs.google.com/uc?export=download&id=0B7lmLLhGZSx5OTVENFlsTkllRTQ Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira

Hausa.naij.ng
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN