Mai taimaka wa shugaba Muhammadu Buhari kan harkokin shafukan sada zumunta Lauretta Onochie, ta ce Allah zai ci gaba da tozarta Pastoci makaryata wadanda ke amfani da sunan Allah ba daidai ba.
Wannan ya biyo bayan shan kunya da Pasto Suleiman ya yi bisa wani harsashe da ya yi a baya cewa jam'iyar APC za ta fadi a zaben gwamnan jihar Ekiti, sai ga APC ce ta ci zaben.
A can baya dai Pasto Suleiman ya sha fadan ababe da ya ce zasu faru amma sai a gan akasin haka.
Lauretta Onochie ta ce, duk wadannan makaryatan wai su Pasto basu fuskantar Allah kafin su furta kalamansu a kan wasu lamurra, sakamakon haka ta ce Allah zai ci gaba da basu kunya a cikin jama'a.
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/Lq4Z5kPck53Le3ibU9RUnY
Latsa nan domin ka sauke Manhajarmu ISYAKU.APK
https://docs.google.com/uc?export=download&id=0B7lmLLhGZSx5OTVENFlsTkllRTQ
Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com
Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira