Type Here to Get Search Results !

‘Yansanda sun cafke wani dan takarar gwamnan Borno da suke nema,ya rike rigar Atiku don ceton shi


Grema Terrab, wani dan siyasa kuma mai takarar kujerar gwamna a jihar Borno, ya fada komar ‘yan sanda a yau, Talata, bayan hukumar ta dade da bayyana nemansa ruwa a jallo. Jami’an SARS ne suka kama Terrab a wurin wani taron da Atiku Abubakar ya halarta.

Hukumar ‘yan sanda ta ayyana neman Terrab ruwa a jallo bisa zarginsa da taka rawa a wani laifin kisa da aka yi a wurin wani taron siyasa da aka yi a gidansa tun watan Afrilu. A yau ne Mista Terrab ya bayyana a garin Maiduguri tun bayan day a bar garin a watan na Afrilu. Rahotanni sun bayyana cewar Mista Terrab ne da kansa ya sanar da hukumar ‘yan sanda batun kisan, amma duk da haka saida jami’an ‘yan sandan suka kama matar sa tare da tsar eta na tsawon sati biyu. Lamarin day a yi sanadiyar zubewar juna biyu da take dauke da shi .

Fastoci da allunan tallar Mista Terrab a matsayin dan takarar gwamnan jihar Borno a karkashin jam’iyyar PDP sun shiga kowanne lungu da sako na garin Maiduguri. Bayan samun rahotannin zuwansa wurin taron, sai jami’an ‘yan sanda sun yiwa wurin kawanya kuma da bayyanarsa keda wuya suka cika hannu da shi.

Kokarin Mista Terrab na jan hankalin Atiku domin ya cece shi bai samu cika yayinda jami’an tsaron Atikun suka fita da shi daga wurin taron. An hangi Mista Terrab na rike gefen babbar rigar Atiku domin ya hana a tafi da shi. Kazalika duk rokon yaransa domin jami’an ‘yan sandan su sake shi bai samu karbuwa ba.
 


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/Lq4Z5kPck53Le3ibU9RUnY Latsa nan domin ka sauke Manhajarmu ISYAKU.APK https://docs.google.com/uc?export=download&id=0B7lmLLhGZSx5OTVENFlsTkllRTQ Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira

Hausa.naij.ng

Top Post Ad

Below Post Ad

Shiga group dinmu na WhatsApp domin samun labaran mu kai tsaye LATSA NAN
Domin zama Wakilin mu a garin ku LATSA NAN
Domin aiko Sako/Labari/Korafi LATSA NAN
Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN
Domin samun labaranmu a Twitter LATSA NAN