Ruwa ya barnata fiye da hekta 80 na gonakin shinkafa a Fadamar Birnin kebbi

Isyaku Garba | Birnin kebbi | 16-7-2018 | 

An sami anbaliyar ruwa da  ya samo asali sakamakon budewar bakin ruwa daga wuyar Sagaldu, sakamakon haka ruwan suka yi mumunar ta'annati ga gonakin shinkafa kimanin hekta 80 bisa kiyasi a gangaren Ama na Fadama a garin Birnin kebbi. Ruwan sun mamaye muhimman wuraren noma na Kajeka, Wuyan Jema, Maidialu, Kwara Karama, Wurin Sarkin Gwandu Jokolo, ya dauka har zuwa Fakkaradda Ala.

A bangaren filin Sarki kadai, an shuka fiye da buhu 10 na shinkafa kuma yanzu ruwa ya mamaye shinkafar da ta fito.Haka zalika dimbin dukiya ne aka shuka a wannan Fadama, amma sai ga ruwa ya mamaye gaba dayan amfanin gonar, domin idan har wannan ruwa bai jayeba, hakan zai haifar da mumunar sakamako ga amfanin gona na shinkafa da ake sa rai za a samu a Damanar bana a wannan Fadama.

Malam Abubakar Arab, wani Manomi ne a wannan Fadama, ya yi kira ga hukumomi da lamarin ya shafa su kawo agajin gaggawa domin shawo kan wannan ruwa da ya yi ambaliya. Haka zalika shugaban manoman shinkafa na damana a Fadamar, Lima Faruku, shima ya yi kira ga hukumomi da lamarin ya shafa su gaggauta kawo dauki domin ceton amfanin gona da ke kan hanyar salwanta matukar ba a tsayar da wannan ruwa ba.

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/Lq4Z5kPck53Le3ibU9RUnY Latsa nan domin ka sauke Manhajarmu ISYAKU.APK https://docs.google.com/uc?export=download&id=0B7lmLLhGZSx5OTVENFlsTkllRTQ Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN