• Labaran yau


  Kebbi: Yadda ruwa ya shafe gonaki a Saminaka da kewaye a karamar hukumar Shanga

  Sani Musa Saminaka | Shanga L.G| 16-7-2018

  Ruwan sama tamkar da bakin kwarya ranar Lahadi ya yi sanadin cikewar Gulbin garin Saminaka, Wawa, Ganwo, Raha da kuma Dugu a yankin karamar hukumar Shanga na jihar Kebbi. Wannan lamarin ya yi sanadin shafewar gonakin gero, Masara, Dawa, Shinkafa da sauran amfanin gona sakamakon ruwa da ya mamaye gonakin.

  Haka zalika wakilinmu na garin Saminaka ya tabbatar mana cewa hatta wasu gonakin Ayaba sun bi ruwa. 

  Wani dattijo mazauni garin Wawa, Malam Garba Layin Gehe, ya shaida mana cewa an taba samun irin wannan ibtila'i fiye da shekara goma da suka gabata a wannan gari.

  Kawo yanzu dai babu labarin rushewar gidaje ko salwantar rayuwa, amma dimbin kayakin amfanin gona sun salwanta a wannan lamari.

  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/Lq4Z5kPck53Le3ibU9RUnY Latsa nan domin ka sauke Manhajarmu ISYAKU.APK https://docs.google.com/uc?export=download&id=0B7lmLLhGZSx5OTVENFlsTkllRTQ Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Kebbi: Yadda ruwa ya shafe gonaki a Saminaka da kewaye a karamar hukumar Shanga Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama