Jihar Kebbi karkashin 'dan Bagudu, albashin ma'aikata da yan pansho ba bashi

Isyaku Garba | Birnin kebbi | 19-7-2018 |


Gwamnamnatin jihar Kebbi karkashin jagorancin Sanata Atiku Abubakar Bagudu ta taka rawar gani wajen kasancewa cikin jerin jihohin Najeriya da suka tsare mutuncin kansu tare da na ma'aikatan jiharsu wajen biyan albashin ma'aikata a kan kari.ISYAKU.COM na da tabbacin cewa babu ma'aikacin jihar Kebbi da ke bin Gwamnati bashin albashi, matukar dai ba matsala ta Banki ko kuskuren wasu takardu ba.

Bincike da muka gudanar sakamakon biyan albashin watan Yuli (July) tun ranar 16 ga wata, ya nuna cewa hakan ya haskaka zukatan ma'aikatan jihar Kebbi, dubi da yadda har ranar Alhamis ATM na Bankuna na cike da ma'aikatan jihar Kebbi da suka shiga layi domin zarar albashinsu.

A tattaunawar mu da wata ma'aikaciyar gwamnatin jihar Kebbi da bata son mu saka hoto ko sunanta a wannan labari, ta ace " Tabbas Gwamna Atiku mutum ne mai kyaun hali, kuma mai yin aiki da ilimi a lokacin da yin haka ya dace,ai ya san an biya albashin watan Juli (June) da wuri domin shagalin Sallah karama, ka gan yanzu babu kudi a hannun ma'aikata, kuma sai ga albashi tun yanzu. Wallahi Atiku ya yi amfani da iliminsa kuma Allah ya kareshi ya biya masa bukatarsa".

Jihar Kebbi dai ta nisanta da sauran jihohi kamar su Kogi, wacce har ma'aikata suna kashe kansu sakamakon rashin biyan albashi na wata da watanni.Wasu kafofin watsa labarai sun ruwaito cewa ma'aikata da dama sun rataye kansu har suka mutu, a lokaci daban daban a jihar Kogi sakamakon bakin cikin rashin biyan albashi, kuma ga dimbin lalurorin gida. Haka zalika da yawa daga cikin makarantun kudi na jihar Kogi sun yi waje rod da yawancin daliban iyalan ma'aikatan gwamnatin jihar Kogi sakamakon rashin biyan albashi.

Haka zalika a jihar Ekiti, akawai zargi mai karfin gaske cewa, gwamnatin jihar bata biya ma'aikata albashinsu ba har na tsawon wata fiye da takwas, wannan ya taka rawar gani sosai wajen faduwar jam'iyar PDP a lokacin zaben Gwamna da aka yi a jihar ta Ekiti a mako da ya gabata.

Domin tabbatar da adalci da shugabanci mai nagarta, Gwamana Bagudu ya shaida ma jama'ar jiharsa cewa "Yan jarida su bincika nawa jihar Kebbi ke samu a kowane wata daga gwamnatin tarayya, kuma nawa ake kashewa wajen biyan albashin ma'aikatan gwamnatin jihar Kebbi" Gwamnan ya yi wannan jawabi ne a ranar 25 ga watan Ramadana, yayin budin baki tare da 'yan Social Media na jihar ta Kebbi a gidan Gwamnatin jiha.

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> whatsapp://chat?code=41x2TuRqdVQ9PrcrucqpTu Latsa nan domin ka sauke Manhajarmu ISYAKU.APK https://docs.google.com/uc?export=download&id=0B7lmLLhGZSx5OTVENFlsTkllRTQ Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN