"Ka fallasa sunayen masu daukan nauyin kashe kashe domin mu yi masu ruwan duwatsu"

Wasu manyan yan adawa da gwamnatin shugaba Buhari, watau Adebanjo da Clark, sun kalubalanci shugaba Buhari akan matsayinsa na cewa yan siyasa ne da basu kaunar manufofin sa su ne ke haddasa kashe-kashe a fadin Najeriya domin su shafa wa gwamnatinsa kashin kaji.

Amma fa Adebanjo cewa ya yi " idan har shuga Bhuhari ya san yan siyasa da ke haddasa wadannan kashe-kashe ai sai ya fallasa su domin mu yi masu ruwan duwatsu.

Idan kuma Buhari ya nace a zancensa, lallai wadanda ke cewa ya rude sun yi gaskiya kenan".

Shugaban na kungiyar Dattijan Yarbawa zalla na Afenifere ya ce " gwamnatin Buhari ta rude, ta yaya zai ce yan siyasa ne ke daukan nauyin makiyaya domin su kashe jama'a a garin Agatu, Enugu, Adamawa da Taraba, shin su waye wadannan yan siyasa ?".

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/Lq4Z5kPck53Le3ibU9RUnY Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN