APC za ta yi nasara a 2019, da R-APC ko babu su - Oshiomhole


Shugaban jam’iyyar APC na kasa ya ce jam’iyyar zata yi nasara a 2019 koda kuwa kungiyar aware na sabuwar APC ta balle.

Kungiyar R-APC wacce ta billo a makon da ya gabata na samun jagoranci daga Galadima, tsohon sakataren jam’iyyar Congress for Progressive Change (CPC). Kungiyar wacce ta bayyana kanta a matsayin APC na “gaskiya” na da goyon bayan shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki, kakakin majalisar wakilai Yakubu Dogara da kuma tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Kwankwaso, sannan kuma akwai sauran jiga-jigan APC da dama.

Mambobin kungiyar na R-APC, sun hada da mutanen jam’iyyu daban-daban da suka hade don kafa APC ciki harda CPC, ANPP da kuma N-PDP.

Oshiomhole ya ce ya fara tattaunawa da mambobin kungiyar dake da korafi mai ma’ana, don haka za su iya share Buba Galadima.
 

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/Lq4Z5kPck53Le3ibU9RUnY Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira

hausa.naij.ng
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN