Kasar Saudiya ta fille kan wasu mutum 7 tare da yan kasar Tchadi

Kasar Saudiya ta fille kan wadanda ke jiran mutuwa bayan an zartar masu da hukuncin kisa sakamakon samunsu da laifukan kisan kai ko sayar da miyagun kwayoyi da suka jibanci hodar iblis da sauransu a cikin kasar. 

Kimanin mutum 73 ne aka kashe su ta hanyar fille masu kai da takobi a kasar ta Saudiya cikin wannan shekara.

Kampanin dillancin labarai na SPA ta ce cikin wadanda aka kashe har da wasu yan kasar Tchadi guda uku da wasu yan kasar Saudiya da suka sace wani dan kasar Pakistan suka kashe shi. Yayin da aka kashe wasu yan kasar Lebanon da suka shiga kasar ta Saudiya da wasu miyagun kwayoyi Captagon.

Shi kuma wani dan kasar Saudiya, fille kanshi aka yi sakamakon banka ma wani mutum wuta, lamari da yayi sanadin mutuwar wannan mutum.

A shekara ta 2016, Saudiya ta fille kan mutane 153, haka zalika a wani kisa da ya ja hankalin Duniya ranar 2 ga watan Janairu, lokacin da Saudiya ta fille kan wani shehun Malami Sheikh Nimr Baqir ql-Nimr tare da wasu mutum 46, duk da kiraye kiraye da kasashen Duniya suka yi ta yi a kan a saki wannan shehun Malami, amma Saudiya ta yi biris da kiraye kirayen,.

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/Lq4Z5kPck53Le3ibU9RUnY Latsa nan domin ka sauke Manhajarmu ISYAKU.APK https://docs.google.com/uc?export=download&id=0B7lmLLhGZSx5OTVENFlsTkllRTQ Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN