Real Sani Twoeffect | Yawuri | 29-7-2018 |
Gwaunan Jahar Kebbi Sanata Abubakar Atiku
Bagudu ya samarda Taranfomomi
Guda Uku (3) ga Al'ummar yankin Karamar Hukumar Mulki ta Yawuri dake
Jahar Kebbi.
Wannan yana daga cikin irin namijin kokarin da Gwamnan yake yi na ganin an wadata yankunan jahar baki daya da wutar lantarki
Sudai wadannan Taranfomomi guda uku za'a sakasu a unguwanni daban-daban dake yankin karamar hukumar ta Yawuri.
Da yake Jawabi, shugaban karamar hukumar mulki ta Yawuri, Alhaji Musa Mohammed (Stone) yace:
"Gwaunatin Mai girma Gwaunan Jahar Kebbi Sanata Abubakar
Atiku Bagudu a shirye take wajen Samar da cigaban Jama'a a kowani lungu
da sako na jahar, shiyasa a koda yaushe batayin kasa a guiwa wajen Samar
da ababen more rayuwa ga Al'ummar jahar"
Ya kuma kara da cewa; "tabbas wasu yankuna na karamar
hukumar suna cikin matukar bukatar Taranfomomin domin samun
wadatacciyar wutar lantarki a yankunan, saboda haka ne Gwamnan Jahar
bai yi kasa a guiwa ba wajen kawo dauki ga Al'ummar wadannan
yankunan".
Haka zalika, shugaban karamar hukumar yace, wannnan abu da
maigirma Gwamnan yayi ya cancanci a yaba masa matuka da gaske, saboda
ya yi godiya ta musamman ga Gwamnan tare da kara mika kokon bararsa ga
Gwamnan a kan sake samun wasu ayyukan na alheri a yankin.
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> whatsapp://chat?code=41x2TuRqdVQ9PrcrucqpTu
Latsa nan domin ka sauke Manhajarmu ISYAKU.APK
https://docs.google.com/uc?export=download&id=0B7lmLLhGZSx5OTVENFlsTkllRTQ
Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com
Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira